ABNA24 : Shafin yada labarai na Misri Alyaum ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar Aljeriya sun sanar da cewa, sakamakon bullar cutar corona nau'in Delta a kasar wannan hakan ya tilasta rufe masallatan kasar.
Minista mai kula da harkokin addini a kasar ta Aljeriya ya bayyana cewa, sakamakon yadda cutar ta bulla da karfinta, an rufe dukkanin masallatai a jihohi 35 daga cikin jihohin kasar.
Baya ga haka kuma tun a ranar Lahadi da ta gabata ce dai gwamnatin kasar ta sanar da daukar kwararan matakai na tunkarar wannan annoba.
Daga cikin matakan har da rage yawan ma'aikata a dukkanin wuraren ayyukan na gwamnati da ma wadanda na gwamnati ba.
Kamar yadda kuma aka tilasta saka takunkumin fuska ga kowa, da kuma kiyaye tazara, gami da fesa maganin kashe kwayoyin cuta a dukkanin wuraren da ake hada-hadar jama'a.
342/